Monday, December 9
Shadow

Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce mambobinta sun kammala cimma matsaya domin fara siyan tataccen man fetur daga matatar man Dangote kai tsaye.

Sun bayyana haka bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta domin bin bahasin yarjejeniyar da suka cimma da matatar da kuma hanyoyin samun man cikin sauki.

Alhaji Zarma Mustapha, wani jigo a ƙungiyar ta IPMAN ya shaidawa BBC shirin da suka yi bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin matatar a ranar litinin, inda ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai haifar da wadatan man fetur a duk faɗin ƙasar.

”Ina bayar da tabbacin cewa muddin muka fara sayen mai kai-tsaye daga Dangote, ba za a rika samun ƙarancin man fetur a ƙasar nan ba, kuma muna sa ran cewa matatan gwamnati ma za su fara aiki nan bada jimawa ba”, In ji shi

Karanta Wannan  Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu'amulla da bankuna - CBN

Alhaji Zarma Mustapha, ya ƙara da cewa, ƙungiyar ta na sa ran cewa za su man fetur da sauki daga matatar ta Dangote, domin a cewarsa a matsayinsu na ƴan kasuwa dole ne su bi yadda za su sami riba kuma samun man da sauki na cikin abubuwan da za su tabbatar da hakan.

Ya ce har yaila yau akwai mabobin ƙungiyar da za su ci gaba da sayen mai daga Kamfanin NNPC, muddin za su same shi da sauki, amma ba zai iya bayar da tabbaci kan yadda farashin man zai kasance a kasuwa ba

Ya ce” Maganan farashi dai ba zan iya cewa komai a kan yadda za ta kasance ba saboda kasuwa ce za ta tabbatar da haka, yadda muka samu a kasuwa shi zai tabbatar da ko akan nawa ne za mu sayarwa jama’a.”

Karanta Wannan  Hoto: An kama matar aure, Balkisu Sulaiman da yaron mijinta ya mata ciki bayan ta haihu ta yadda dan a kwata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *