
Bayan jan ƙafa na tsawon lokaci, ɗaya daga cikin ƴan majalisar dattawa na jam’iyyar NNPP Sanata Abdurahman Kawu Sumaila ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Matakin na zuwa ne bayan shafe watanni ana takun saƙa tsakanin Sanatan da jam’iyyarsa ta NNPP a jihar Kano.
A makon da ya gabata ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci wata tawagar yanmajalisar tarayya na NNPP inda suka gana da shugaban jam’iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Kano.
A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakin ne domin samar da ci gaba ga al’ummar mazaɓarsa.
Ya ce ”Wasu daga cikin dalilan da za su sa mu fice shi ne yankin da muka fito. Ya za mu iya samar wa mutanen yankin mu wani abu da zai amfanar da su, kuma ai ita siyasa da ƙunshi tattaunawa domin nema wa al’umma maslaha.”
Sanatan ya kuma yi watsi da batun cewa ya yi wa jam’iyyar NNPP butulci ganin cewa a ƙaƙashin inuwarta aka zaɓe shi inda ya yi nuni da cewa akasarin ƴan siyasa 109 da suka tsaya zaɓen majalisar dattawa a jam’iyyar ba su kai labari ba.
”Ai ba wai NNPP ɗin ba ce, waye ya tsaya a cikin NNPP ɗin,saboda haka ai zaɓa ta da aka yi kowa ya san an zaɓe ni ne saboda ni ne ɗantakaran, kuma a zone ɗin ai da sun tsaya, me ya sa ba su ci ba, sai yanzu? Saboda haka suna yana da tasiri.” in ji shi
Sanatan ya ƙara da cewa barinsa jam’iyya ba ta na nufin an ja zare tsakaninsa da gwamnatin NNPP a jihar Kano ba ne, inda ya ce a shirye ya ke ya goyi bayan duk wani shirin da gwamnatin za ta ɓullo da shi wanda zai kawo ci gaba ga al’umma.