
Yaronnan dan jihar Anambra wanda aka ruwaito ya dirkawa mata 10 ciki a cikin watanni 5 yayi bayani dalla-dalla game da irin dabarar da yake amfani da ita wajan yaudarar matan suna yadda dashi.
Yaron mai shekaru 18 an daukoshi daga kauyene aka kaishi wajan wani dan kasuwa dan ya koya masa kasuwanci.
Saidai yaron ya dirkawa diyar me gidan ciki sannan ya dirkawa yarinyar shagon me gidan nasa ciki.
Megidan ya koreshi inda ya mayar dashi kauye, saidai watanni biyu bayan mayar dashi kauyen, a camma ya dirkawa mata 8 ciki.
Kwamishiniyar mata da walwala ta jihar Anambra, Ify Obinabo tace mahaifiyar yaron ce da kanta ta kaishi kara wajenta. Tace abin ya bata mamaki dan hakane ma ta kira yaron take tambayarsa shin wai yana da wani lakani ne ko Asiri da yake amfani dashi wajan yaudarar mata suna yadda dashi?
Sai yaron ya kada baki yace ko daya, yace kawai yana gayawa matanne cewa yana sonsu sosai kuma zai auresu idan ya samu kudi, sai du yadda dashi.