
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu sauki a gyaran da yake yiwa ‘yan Najeriya, dolene dama sai an sha wahala.
Yace kuma tun kamin ya hau mulki an san da wannan.
Yace kuma ba ma shine ya fada ba, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne ya fada a wani taro a Kaduna.
Yace amma duk da haka an samu masu son hambarar da gwamnatinsa.
Manyan sabbin tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta kawo sune cire tallafin man fetur da na dala.