
Ba Zan Yi Musayar Yawu Da Nasir El-Rufai Ba, Cewar Nuhu Ribadu
“An ja hankalina zuwa ga hirar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi da kafar yada labarai da yammacin ranar Litinin.
Da ba don gudun kada na yi shiru a gaskata maganganunsa ba, da na yi watsi da shi. Saboda na fi shagaltuwa da tarin aiyukan da ke gabana,fiye da tanka ire-iren su Nasir El-Rufai a kafafen yada labarai.
Duk da cin zarafi da aibata ni da Nasiru yake yi, hakan bai sa na taba fadin wani mummunan abu akansa ba a ko’ina. Ba don komai na ki aibata shi ba sai don mutunta zumuncin da ke tsakaninmu da kuma abotar mu ta baya, don haka abinda ban yi tun a baya ba, ba zan fara yanzu ba.
Sai dai ina kira ga jama’a da su yi watsi da ikirarin El-rufai akaina
Bari na kankare muku shakku in fadi da babbar murya cewa ban taba tattauna batun ko zan yi takarar shugabancin kasa a shekarar 2031 da kowa ba, domin hankalina da gangar jikina sun ta’allaka ga aikina na ganin ci gaban Najeriya da nasarar gwamnatin shugaba Tinubu.
Don haka ina rokon Nasir El-Rufai da ya bar ni na ci gaba da fuskantar aikina na gina kasa kamar yadda ban dame kaina da al’amuransa ba”. Nuhu Ribadu
Me zaku ce ?