
Dan gidan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana cewa tunda jami’an tsaro suka kama mahaifinsa, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yaki musu magana.
Yace abinda kawai mahaifinsu ke gayawa jami’an tsaron shine idan suna da wani abu da suke zarginsa dashi, su kaishi kotu.
Yace shirun da mahaifin nasa yayi yasa jami’an tsaron na bayyana hakan da rashin basu hadin kai, yace amma kundin tsarin mulki kasa ne ya baiwa mahaifin nasa wannan dama.
Yace dalili kenan ma da yasa ICPC din suke shirya karya suna jinginawa mahaifin nasa.
Hakan na zuwane bayan da ICPC suka ce sun gano na’urar yiwa waya kutse a cikin gidan Nasiru El-Rufai.
Saidai Tuni iyalan Malam Nasiru suka fitar da sanarwa inda suka karyata hakan.
Itama Matar Malam Nasiru, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai tace a gabanta aka binciki gidan mijin nata amma maganar gaskiya babu wata na’urar yiwa waya kutse da aka gano.