
Dan majalisar wakilai, Hon. Sagir Ibrahim Koki ya bar jam’iyyar NNPP.
Ya sanar da hakanne a wata sanarwa da ya fitar ranar 11 ga watan Nuwamba inda yace yana godiya da damar da jam’iyyar ta bashi yayi takara a cikin ta.
Saidai yace dalilin na barin jam’iyyar, Rikicin Cikin gidane wanda ya hanashi gudanar da ayyukan wakilci da aka zabeshi akansu.
Zuwa yanzu dai bai bayyana jam’iyyar daya koma ba.