Friday, December 5
Shadow

Dangote zai rage farashin man fetur dinsa daga Naira N865 akan kowace lita zuwa Naira N841 a Legas da sauran Jihohin Yarbawa, Sannan A Abuja da jihar Kwara da Edo, ma zai rage farashin man zuwa Naira 851 kan kowace lita

Matatar man fetur ta Dangote zata rage farashin man fetur dinta zuwa daga Naira 865 zuwa Naira 841 akan kowace lita a jihar Legas da sauran Jihohin Yarbawa.

Hakanan matatar zata rage farashin kowace lita zuwa Naira 851 a Abuja da kuma jihohin Kwara, da Edo.

Hakan na zuwane a yayin da Matatar man ta Dangote ke shirin fara kaiwa gidajen sayar da man fetur man kyauta da motocin tanka na dakon Man fetur din data siyo daga kasashen waje.

Rikici tsakanin matatar man fetur ta Dangote da sauran ‘yan kasuwar man fetur ya ta’azzara sosai inda suka ce sai ya shiga kungiyarsu amma shi kuma yace hakan ba zata yiyu ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Wallahi 'yan Tiktok ko ba zaku iya kama gida a Abuja ba, ko Kaduna ce ku je ku maqale, dan Kano ba wajan zamanku bane>>Gfresh Al-amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *