
Rahotanni sun bayyana cewa, Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar Canji.
Rahotannin yanda kasuwar ta kasance a ranar Laraba na cewa, an sayi dala akan Naira N1,549.26 wanda hakan ya nuna darajar Nairar ta fadi idan aka kwatanta da yanda aka sayi dalar akan Naira N1,549.04 a ranar Talata.
Nairar ta rasa darajar Kwabo N0.22.
Wannan farashin kasuwar Gwamnati ne.
A kasuwar ‘yan bayan fage kuwa Dalar an saye ta ne akan Naira N1,590 a ranar Laraba inda hakan ke nuna darajar Nairar ta dan tashi da Naira 5 idan aka kwatanta farashin da aka saye ta na Naira N1,595 a ranar Talata.