Friday, July 17
Shadow

Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar Canji

Rahotanni sun bayyana cewa, Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar Canji.

Rahotannin yanda kasuwar ta kasance a ranar Laraba na cewa, an sayi dala akan Naira N1,549.26 wanda hakan ya nuna darajar Nairar ta fadi idan aka kwatanta da yanda aka sayi dalar akan Naira N1,549.04 a ranar Talata.

Nairar ta rasa darajar Kwabo N0.22.

Wannan farashin kasuwar Gwamnati ne.

A kasuwar ‘yan bayan fage kuwa Dalar an saye ta ne akan Naira N1,590 a ranar Laraba inda hakan ke nuna darajar Nairar ta dan tashi da Naira 5 idan aka kwatanta farashin da aka saye ta na Naira N1,595 a ranar Talata.

Karanta Wannan  Ni Dai Ban San Inda Sauran 'Yan Matan Fim Suka Samo Na Su GLK Din Ba, Amma Ni Tawa Baby Na Ne Ya Siya Min, Inji Samha M. Inuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *