
Dan majalisar Amurka, Riley M. More dake zuga shugaban kasar Amurka, Donald Trump akan Najeriya yace ‘yan mata ‘yan makaranta da aka yi garkuwa dasu a jihar Kebbi garin Kirista ne.
Hakan ya jawo masa suka da Allah wadai.
Daya daga cikin wadanda suka mayar masa da martani, akwai tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad inda yace garin da aka sace daliban ba garin Kirista bane, garin musulmi ne kuma daliban ma musulmai ne.
Kasar Amurka dai ta sha Alwashin kawo hari dan tallafawa Kiristocin Najeriya bisa zargin cewa, ana musu Khisan Khiyashi.