
Direban motar da ta yi hadari da dan damben Najeriya, Anthony Joshua inda har abokansa 2 suka rasu yace da Anthony Joshua ne ya zauna a gaban motar.
Yace amma daga baya sai yace yana kare masa madubin gefe ya koma baya abokinsa ya dawo gaban motar.
Abokan Anthony Joshua biyu dai duka sun rasu a hadarin inda shi kuma ciwuka ba masu tsanani ba yaji.