
Wani DJ me saka kida, ya dakatar da kida a wajan bikin da ya je bayan da aka hanashi abinci yayin da ake ta baiwa sauran mutanen abinci.
DJ din ya dakatar da kidan sannan ya kashe Janareta dan ya nuna fushinsa.
A wani Bidiyonsa da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga DJ din yana kumfar baki da fadin cewa, ba’a masa adalci ba.
Saidai daga baya an bashi baki inda aka masa alkawarin samar masa da abinci da zai ci.