
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, sabuwar dokar Haraji ba zata yi aiki ba saboda an mata katsalandan.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace duka majalisun tarayya sun amince cewa dokar da suka amince da ita ba itace aka wallafa ba
Atiku yace kuma a doka, idan aka samu irin wannan matsala ta yin kari ko gogewa wani abu daga cikin dokar da majalisar ta amince da ita, dokar ba zata yi aiki ba.
Yace yandu dolene saidai a yi wata sabuwar dokar sannan majalisar ta sake yin zama dan tantancewa da amincewa ko rashin amincewa da ita.