Sunday, July 12
Shadow

Dokar Haraji ba zata yi aiki ba saboda An mata katsalandan, sai an sake yin wata>>Inji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, sabuwar dokar Haraji ba zata yi aiki ba saboda an mata katsalandan.

Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace duka majalisun tarayya sun amince cewa dokar da suka amince da ita ba itace aka wallafa ba

Atiku yace kuma a doka, idan aka samu irin wannan matsala ta yin kari ko gogewa wani abu daga cikin dokar da majalisar ta amince da ita, dokar ba zata yi aiki ba.

Yace yandu dolene saidai a yi wata sabuwar dokar sannan majalisar ta sake yin zama dan tantancewa da amincewa ko rashin amincewa da ita.

Karanta Wannan  A karin farko, 'yan majalisar wakilai sun murza gashin baki inda suka cewa, shugaba Tinubu ko dai ya dakatar da duk wani shirin siyasa da yakin neman zabe ya magance matsalar tsaro, ko kuma ya sauka kawai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *