Wednesday, January 15
Shadow

Domin Kawo Saukin Hauhawar farashin kayan masarufi, Gwamnati zata cire harajin VAT akan kayan abinci da ake shigowa dasu Najeriya

Domin kawowa al’umma saukin rayuwa, Gwammatin tarayya ta sanar da shirin cire harajin VAT daga shigo da kaya da hukumar Kwastam ke karba akan kayan abinci na tsawon watanni 6.

Gwammati zata dauki wannan mataki ne dan magance matsalar hauhawar farashin kayan abinci.

Yanzu haka an aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da rahoto kan wannan lamari dan ya duba ya saka masa hannu.

Kayan da za’a cirewa harajin sun hada da kayan abinci, magunguna, abincin kaji, Fulawa da sauransu.

Da yawan ‘yan Najeriya dai na kukan tsadar rayuwa, abin jira a gani shine idan wannan mataki zai haifar da da me ido.

Karanta Wannan  Kungiyar 'yan kasuwar man fetur, IPMAN ta yi baranzanar tsayar da aiki saboda karin kudin man feturninda tace hakan ya kara jefa 'yan Najeriya wahala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *