DPO na ofishin ‘yansanda dake Ijanikin a CSP Bolaji Olugbengajihar Legas ya mutu.
Rahotanni sun ce yana zaune a ofishinsa kawai ya yanke jiki ya fadi ya mutu tun kamin a kaishi Asibiti.
Tuni dai aka kai gawarsa zuwa Mutuware. Lamarin ya farune ranar 17 ga watan Oktoba.
Zuwa yanzu dai hukumar ‘yansandan bata ce uffan kan lamarin ba.