fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Rayuwar Sayyadina Umar Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci

Cikakken Sunansa da Asalinsa

Sunansa Umar Dan Khaddabi Dan Nufail Dan Abdul Uzza Dan Rayahi Dan Abdullahi Dan Kurdi Dan Razahi Dan Adiyyu Dan Ka’abu Dan Lu’ayyu Dan Galibu al Adawi al Kurashi. Ya hadu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a zumunci ta wajen kakansa na Takwas, wato Ka’abu Dan Lu’ayyu, wanda shi ne kakan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na bakwai.

Mahaifiyarsa ita ce Kanwar Abu Jahli, Hantamah diyar Hisham Dan Mughirah daga kabilar Makhzum.

Haifuwarsa:

An haifi Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu bayan yakin nan da aka fi sani da Harbul Fijar, a shekara ta Arba’in da uku kafin hijira. Don haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya girme shi da shekaru goma cif.

Siffarsa da Dabi’unsa:

An siffanta Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu da cewa, mutum ne dogo, kakkaura, mai sanko a kansa. Ga shi kuma jawur yake kamar kwara. Saboda tsawonsa idan ka hango shi daga nesa za ka yi tsammanin mahayi ne.

Game da dabi’unsa kuwa, Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu ya gaji kaushin hali daga mahaifinsa. A lokacin kuruciyarsa ya kasance yana yi wa mahaifin nasa kiyon rakuma. Mahaifin nasa kuwa yana wahalar da shi sosai, yana kuma dukansa idan ya saba masa.

Mahaifin Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu, al Khaddabi ya kasance yana wahalar da kaninsa Zaidu, musamman ma lokacin da kanin nasa ya kyamaci bautar gumaka, ya je neman addinin gaskiya na Annabi Ibrahim. Shi kuma Sayyidina Umar ya kan wahalar da Dan baffansa kuma mijin kanwarsa, wato Sa’idu Dan Zaid, musamman a lokacin da ya san ya musulunta tare da matarsa.

Rayuwarsa kafin Musulunci:

Muna iya raba rayuwar Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu gida biyu: kashi na farko ya yi shi kafin zuwan Musulunci, kashi na biyu kuma a cikin Musulunci. A kashi na farko na rayuwarsa, Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu bai zamo wani mutum mai cikakken muhimmanci ba, duk da yake yana cikin ‘yan majalisa. Amma furta kalmar shahadarsa ke da wuya sai ya koma wani muhimmin mutum wanda rayuwarsa ta ke da muhimmin ambato daga wannan rana har zuwa ranar tashin kiyama.

Sayyidina Umar Radiyallahu Anhu shi ne wakilin kabilarsa ta Banu Adiyyin a majalisar zartaswa ta Kuraishawa wadda ta ke da kujeru goma.

Yadda Musulunci ya Ratsa Zuciyarsa:

Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya musulunta a shekara ta biyar kafin hijira, bayan talakawan Musulmai sun sha wuya sosai a hannunsa. To, ya aka yi ya musulunta? Wane irin sirri ne ya karya zuciyarsa a daidai wannan lokaci?

Tun da farko dai Allah ya yi masa gamon katar ne da addu’ar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin a lokacin da kunci da wahala suka tsananta a kan talakawan Musulmai, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya roki Allah ya karfafi addininsa da daya daga cikin mutane biyu, duk wanda ya fi soyuwa zuwa ga Allah a cikinsu, Sayyadina Umar Dan Khaddabi Radiyallahu Anhu ko kawunsa Abu Jahli Dan Hisham. Zabin Allah sai ya fada a kan Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu.

Farkon bayyanar tasirin wannan addu’a shi ne lokacin da wa su raunanan Musulmai za su yi hijira zuwa Habasha, sai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya gamu da su. Sai ya tambayi Ummu Abdullahi Radiyallahu Anha diyar Hantamah ina su ka nufa? Sai ta ce masa, za mu bar mu ku garinku tun da kun kuntata mana, kun hana mu ‘yancin mu yi addinin da muka zaba, kun hana mu sakat kamar mu ba ‘yan gari ba ne. Za muje in da za mu samu sauki da kwanciyar hankali tun da kasar Allah fadi gare ta. Da ta gama fadin wannan magana sai Sayyadina Umar ya ce, Allah ya kai ku lafiya!

Wannan addu’a ta Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ta bai wa kowa mamaki, domin ba a san shi da tausaya wa Musulmai ko kadan ba. Da Ummu ta fada ma Amiru Dan Rabi’ah abin da ya faru, sai ya ce mata, hala kina zaton Umar ya musulunta? Sai ta ce, eh, don na ga ya tausaya mana sosai sabanin al’adarsa. Amiru ya ce, to sai in jakin gidansu ya musulunta!

Ana cikin haka ne wata rana Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya shiga Masallacin ka’aba domin ya yi dawafi ya gaida iyayen gijinsa, sai ya hadu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana Sallah. A wannan lokacin sai ya dan mayar da hankali domin ya ji abin da Manzo yake karantawa. Aka yi dace kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana karanta suratul Hakkah, sai karatun ya kama shi sosai har ya ce, wallahi Kuraishawa sun yi gaskiya da suka ce mawaki ne. Amma wallahi wakarsa tana da dadi. Bai rufe bakinsa ba sai Manzon Allah ya kawo in da Allah ke cewa:

Karanta wannan  Kwalejin kimmiya da fasaha ta YABATECH ta hana dalibai sanya slippers zuwa makaranta

“To, ba sai na yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba. Da abin da ba ku iya gani. Lalle ne, shi (Alkur’ani) tabbas maganar wani Manzo mai daraja ce (Jibrilu AS).”

Da Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ji haka sai ya ce, to in ko haka ne boka ne kenan. Sai ya ji ance:

“Kuma shi ba maganar boka ba ne. Kadan kwarai za ku iya tunawa. Abin saukarwa ne daga Ubangijin halitta duka.”

A nan sai ransa ya darsa masa cewa, to ko karya ce yake yi? Sai karatun ya ci gaba:

“Kuma da (Manzon Allah) ya fadi wata magana, ya jingina ta gare mu. Da mun kama shi da dama. Sa’an nan, lalle ne, da mun katse masa lakka. Kuma daga cikinku babu wasu masu iya kare (azabarmu) daga gare shi. Kuma lalle ne shi (Alkur’ani) tunatarwa ce ga masu takawa. Kuma lalle ne mu, wallahi, muna sane da cewa daga cikinku akwai masu karyatawa. Kuma lalle ne shi (Alkur’ani) wallahi bakin ciki ne ga kafirai. Kuma lalle shi gaskiya ce ta yakini. Saboda haka, ka tsarkake sunan Ubangijinka, Mai girma.”

Kafin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gama sallah jikin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya yi sanyi sosai, zuciyarsa ta sauya duk yadda ba a zato, amma dai lokacin bai yi ba tukuna.

Bayan kwana uku da musuluntar baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wato Sayyadina Hamza Alaihi Salatu Wassallam, sai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya gamu da wani daga cikin talakawan Musulmai, sai ya fara gaya masa magana mai kaushi kamar yadda ya saba, a lokacin Musulmai sun fara jin karfin yin magana saboda musuluntar Sayyadina Hamza, sai wannan bawan Allah ya kada baki ya ce masa, to, kai Umar ka na wahalar da kanka a kan matsalar da ko a cikin gidanku ba ka magance ta ba! Sayyadina Umar ya ce, wane ne ya karkace a cikin gidanmu? Sai ya ce, kanwarka da mijinta.

Jin haka ke da wuya sai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya fusata ya tasar ma gidan Fatimah diyar Khaddabi. Da ya isa sai ya ji sautin karatun Alkur’ani, amma kafin a bude masa kofa sai da aka boye takardun da ake karatu don gudun fitinarsa. Kafin Fatimah ta gama yin maraba da yayan nata tuni har ya kai ma ta duka yana neman a ba shi abin da ake karantawa. Da suka lura al’amarin nasa babu tausayi ko kadan a ciki, sai kanwarsa ta ce masa, an ki a ba ka, kuma Musulunci ko kana so ko ba ka so sai an yi. Ka yi duk abin da zaka iya!

Nan take sai jikin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya yi sanyi, hankalinsa ya fara dawo masa, ya ji kunyar wannan raini da ya janyo ma kansa daga kanwarsa wadda ta ke ganin girmansa tana mutunta shi. A cikin lumana sai ya nemi karin bayani. Allah Sarki! Kafin marece Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya bi sawun Musulmai.

Daukakar Musulunci Bayan Musuluntarsa:

Musuluntar Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ke da wuya, sai ya nemi a fito da addini sarari, a daina boye shi kamar garar kunya. A wannan ranar ne Musulmai suka fito a cikin garin Makka su kayi wani jerin gwano a karkashin jagorancin Sayyadina Umar da Hamza don su bayyana wa mushrikkai cewa, yanzu fa Musulunci ya samu gata, ya yi shingi ya huta da ratse.

Za’aci Gaba INSHAALLAH.

Daga B Salia Sicey

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.