
Hukumar ‘yansandan Farin kaya ta DSS ta tsare shugaban daliban Najeriya, Atiku Abubakar Isa bayan da ya zargi cewa dan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi Naira Miliyan 100 dan ya goyi babanshi, Bola Ahmad Tinubu amma yakiya.
Atiku ya kuma zargi dan shugaban kasar, Seyi Tinubu da daukar nauyin sawa a masa dukan kawo wuka.
Sahara reporters tace ta samu cewa Atiku na hannun hukumar DSS tun ranar Talata.
Rahoton yace kamen nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bikin rantsar dashi a matsayin shuganan daliban Najeriya inda wasu da ake zargin daukar nauyinsu aka yi suka watsa taron sannan aka kama Atiku aka tursasashi ya janye zargin da yawa dan gidan shugaban kasar.
Rahoton yace yanzu haka Atiku na wani Asibitin DSS a Airport Road inda ake cewa wai yana jinya ne amma maganar gaskiya ana son sai ya janye zargin da yawa dan shugaban kasa, Seyi Tinunu ne.
TRahoton yace An tursasa Isa ya dauki hoto da wata Bindiga da bai da alaka da ita inda ake son ko ya janye zargin da yakewa dan shugaban kasa ko a bata masa suna.