Thursday, May 22
Shadow

DSS ta sake kama dan Gwagwarmaya Mahadi Shehu

Hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta sake kama dan Gwagwarmaya Mahadi Shehu a Kaduna.

Rahoton Daily Trust yace an kama Mahadi Shehu ne a Unguwar Dosa da misalin karfe 11 na safe.

Saidai zuwa yanzu babu karin bayanin dalilin kamashi.

A watan Disambar da ya gabata ne dai aka kama Mahdi Shehu bisa zargin watsa labarin da ba daidai ba.

Na kusa dashi sun bayyana cewa suma basu san dalilin kamen ba.

Karanta Wannan  Duk da Hukumar Hisbah ta Kano tace ta je gidan yarin Goron Dutse ta ga ba gaskiya a zargin Luwadi da ake da yara, Saidai da yawa sun ce basu yadda da binciken na Hisbah ba, ciki kuwa hadda tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *