Friday, February 7
Shadow

Gwamnan Jihar Naija ya bada shawarar a rika amfani da yaren Hausa wajan koyar da yara a makarantun Firamare da Sakandare a jihohin Arewa

Gwamnan jihar Naija, Muhammad Bago ya bayar da shawarar a rika amfani da yaren Hausa wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da Sakandare a jihohin Arewacin Najeriya.

Ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a Minna ranar Talata inda yace daukar wannan mataki zai kara karfafawa yara shiga makaranta.

Yace kamata yayi a rika Amfani da Turanci a matsayin Subject kawai amma ba yaren koyar da karatun ba.

Gwamnan ya jawo hankalin Gwamnonin Arewa dasu canja tsarin karatun yankin dan karfafa gwiwar yara su shiga makaranta.

Karanta Wannan  Tinubu dan uwanmu ne Bayerabe mun fi kowa sanin halinsa shiyasa bamu zabeshi ba a zaben 2023>>Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta magantu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *