
Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya gayawa al’ummar jiharsa da su ci gaba da goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Fubara ya bayyana hakane a sakon Easter da ya fitar inda yace wannan lokaci ne na hadin kai da yin sulhu.
Yace Mutanen jihar su ci gaba da fatan Allah ya kawo ci gaba da warwarewar Al’amura a jihar.