
Jaridar Punchng ta ce ta samu tabbacin cewa an fitar da ministan kudi, Wale Edun zuwa kasar Ingila dan neman magani bayan da ya kwanta rashin Lafiya.
Ministan dai ya kwanta rashin lafiya wanda rahotannin farko suka ce Shanyewar rabin jiki ce amma daga baya, Fadar shugaban kasa ta musanta hakan.
Sannan fadar shugaban kasar tace lallai bashi da lafiya amma ba shanyewar rabin jiki bace, sannan kuma ba’a fitar dashi zuwa kasar waje ba.
Amma jaridar Punchng tace tabbas ta samu sahihin labarin da yace mata An fitar da ministan.
Hakanan rahotanni sun ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon ministan Kudin amma fadar shugaban kasar ta karyata hakan.