
A jiyane Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da cewa ta je gidan gyara hali dake Goron Dutse inda aka yi zargin cewa ana luwadi da matasa da ake tsare dasu dan ta yi bincike.
Hukumar tace ta kammala binciken ta kuma ta gano cewa babu kanshin Gasol a zargin.
Saidai duk da haka wasu sun ce basu gamsu da binciken Hisbah ba, kamata yayi a samu dan jarida wanda bashi da alaka da gwamnati watau me zaman kansa yayi wannan bincike.
Wasu sun ce shin a yayin binciken da Hisbah ta yi an cire wandon yaran an ga yanayin lafiyar duburarsu, kuma an kaiwa likita ya dubasu?
Cikin masu irin wannan ra’ayi hadda Malam Bashir Ahmad wanda tsohon hadimin shugaban kasa ne.
Ya bayar da shawarar a baiwa dan jarida irin su jafar jafar damar zuwa wannan gidan yarin dan yin binciken kwakwaf