Wednesday, December 4
Shadow

Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, me martaba sarkin  Kano, Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a jihar Kaduna.

Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter.

Sani yace Sarki Muhammad Sanusi II yana yakar zalunci a jihar  Kano amma kuma a baya ya goyi bayan zaluncin a jihar Kaduna.

Sarki Sanusi dai abokine a wajan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma a lokacin da aka cireshi daga mukamin sarkin Kano, ya koma Kaduna inda El-Rufai ya bashi waje ya bude fada sannan kuma ya bashi mukami a jami’ar jihar Kaduna.

Karanta Wannan  DAƊUMI-ƊUMI: Ƙungiyar Dalibai Ta Ƙasa Za Ta Gudanar Da Źanga-Źànģa A Ranar 15 Ga Wannan Wata Kan Ƙarin Kuɗin Man Fetur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *