
Wata Kungiyar ‘yan Arewa me suna The Arewa Think Tank (ATT) ta bayyana cewa, abin mamaki duk da kokarin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na sauko da kayan masarufi amma har yanzu babu wanda ya fito yake yabonsa.
Shugaban kungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Kaduna.
Yace tsare-tsaren tattalin arziki na Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na aiki amma duk da haka babu wanda kake ji yana yabonsa sai ma ci gaba da zaginsa da ake yi.
Yace yana baiwa mutane hakuri nan gaba kadan zasu ga ci gaba sosai a harkar mulkin Najeriya.