
‘Yar bautar kasarnan da aka yi garkuwa da ita a jihar Benue, Rofiat Lawal ta shaki iskar ‘yanci.
Rahotanni sun bayyana cewa, an sako ta ne bayan da danginta suka biya kudin Fansa naira Miliyan 1.1.
An yi garkuwa da itane yayin da take kan hanyar zuwa Ibadan jihar Oyo daga Benin Jihar Edo inda zata fara aikin bautar kasar.
Rahoton yace masu garkuwa da mutanen da farko sun nemi sai an biyasu Naira Miliyan 20 amma daga baya suka dawo miliyan 5 bayan mahawara me zafi, a karshe dai hakan ma danginta suka kasa biya.
Daga karshe dai an tattaro Naira Miliyan 1.1 daga ‘yan Uwa da abokan Arziki wanda aka baiwa ‘yan Bindigar.
An sakota a daren ranar Juma’a inda da safiyar ranar Asabar ta hadu da danginta.