
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana cewa, duk rintsi suna tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Ta bayyana hakanne a shafinta na sada zumunta.
Hakan na zuwane bayan da aka zargi shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kiran sunan Tinubu ba tare da hadawa da Kashim Shettima ba a wajan yakin neman zabe.
Lamarin ya jawo hatsaniya wanda da kyar aka fitar da Gandujen daga wajan taron.