
Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana cewa duk wani dan siyasar Arewa da ya taba rike mukami a cikin shekaru 20 da suka gabata, yana da hannu wajan lalacewar yankin.
Yace matsalar Arewa ba a cikin shekaru 2 da suka gabata ta fara ba, ta dade ana fama da ita.
Ya kara da cewa, kuma duk wani dan siyasa da ya taba rike mukami a yankin ya kamata ya fito ya baiwa mutane hakuri saboda sun gaza.
Yace a lokacin Mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya saki kudi sosai na tallafi yace amma da yake in dambu yayi yawa baya jin mai, hakan bai kawo karshen matsalar ba.
Uba Sani yace mutane su yi hankali da ‘yan siyasar da ana tare dasu a baya amma su rika warewa suna cewa wai su sun tuba.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Trust TV.