Sunday, March 23
Shadow

Ina alfahari da babana, ‘Yan hassada ne ke son bata masa suna>>Inji Dan Tsohon Shugaban kasa, Janar Sani Abacha

Dan tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha me suna Sadiq ya jinjinawa mahaifin nasa inda yace yana alfahari dashi.

ya bayyana hakane a yayin da aka taso da guguwar sukar mahaifin nashi.

Yace yawanci masu sukar mahaifin nashi suna yi ne saboda hassada da kuma wadanda suka ci amanarsa.

Yace amma mahaifinsu shugaba ne na gari kuma yayi abinda ya kamata a kasarnan.

Guguwar Sukar Janar Sani Abacha ta sake tasowane biyo bayan kaddamar da littafin da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi.

Karanta Wannan  Sowore ya baiwa 'yan Najeriya shawarar su je su shiga gidaje 753 na Abuja da gwamnati ta kwace saboda nasu ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *