
Hukumar hana rashawa da cin hanci, EFCC ta kwato Naira Biliyan 5 da Dala Miliyan $10 daga hannun tsaffin ma’aikatan NNPCL da ‘yan Kwangila.
Wadannan kudade na da alaka da gyaran matatun man Kaduna, Fatakwal, da Warri.
Hakanan kuma Punchng tace ta samu karin bayanin cewa, EFCC din na kokarin kara kwato wasu Naira Biliyan 10 da wasu dala Miliyan $13 da suma aka karkatar dasu.
Rahoton yace shugaban EFCC, Ola Olukoyede da kansa ne ke jagorantar wannan bincike musamman ganin yanda aka kashe makudan kudade wajan gyaran matatun man Najeriya amma har yanzu basa aiki.
Gwamnatoci da suka shude sun yi kokarin gyaran matatun man fetur din amma basu yi nasara ba.