Monday, June 2
Shadow

El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya

YANZU-YANZU: El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya.

An hango tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, na tattaunawa da ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, a gefen taron shekara-shekara karo na 11 na Cambridge Africa Together Conference (ATC), wanda ke gudana a Jami’ar Cambridge, ƙasar Birtaniya.

Taron, wanda ke ɗaya daga cikin manyan taruka da ke haɗa shugabanni, masana da matasa daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka da duniya, ya kasance dandali na musayar ra’ayoyi, tattaunawa kan ci gaban Afirka, shugabanci da sabbin dabaru na magance matsalolin da ke fuskantar nahiyar.

El-Rufai da Peter Obi, wadanda dukkansu sanannu ne a harkar siyasar Najeriya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da kafafen watsa labarai.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya dawo Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *