
Wata Kungiyar Arewa ta bayyana cewa, Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na son kawo rudani a kasarnan.
Kungiyar me sunan Arewa Think Tank (ATT) ta bayyana cewa Ba gaskiya bane da El-Rufai ke cewa mutanen Arewa na cike da fushi kan mulkin Tinubu, ta kara da cewa, El-Rufai din ne dai ke son kawo rudani kawai.
Kungiyar ta bayyana hakane ta bakin shugabanta, Muhammad Yakubu da aka yi hira dashi a gidan Talana AIT.
Ya bayyana cewa, lamarin zaben 2027 da El-Rufai ke magana akai yana son shiga hurumin Allah ne inda yace Allah ne kadai yasan waye zai kai shekarar 2027 din.
Ya kuma musanta zargin da El-Rufai yayi na cewa, Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a shekarar 2031.