Tuesday, April 14
Shadow

Kotu ta daure matashi da ya saci Kaza

Kotun Magistrate dake Ago Iwoye, a jihar Ogun ta daure wani matashi me suna Adebanjo Segun dan kimanin shekaru 21 saboda satar kaza.

Kakakin Hukumar NSCDC na jihar, Dyke Ogbonnaya ne ya sanar da hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Laraba.

Lamarin ya farune ranar Laraba, February 19, 2025 inda aka kama matashi Adebanjo.

Ogbonnaya ya bayyana cewa, Matashin ya taba aikata hakan a watan Disamba na shekarar 2024 amma aka yafe masa da tunanin cewa shine na farko da ya taba aikatawa.

Yace amma a wannan karin an gurfanar dashi a kotu inda kotun ta yanke masa hukuncin daurin watanni 6.

Karanta Wannan  Kalli Hoton Sabon Salon Rashin Imani yanda 'yan Bìndìgà suka fara yankewa wanda suka yi garkuwa dasu hannu idan ba'a kai kudin fànsà ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *