Tsohon Kwamishina a jihar Kaduna lokacin mulkin tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, watau Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu da yanzu haka yake tsare bisa zargin satar kudaden gwamnati, yace Gwamna El-Rufai ne ya sashi duk abinda yayi.
Ya bayyana hakane a cikin jawabin da ya baiwa ‘yansanda bayan kamashi, kamar yanda wani dansanda da baiso a bayyana sunansa ya gayawa manema labarai kamar yanda jaridar TheNation ta ruwaito.
Ana zargin Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu da sayar da daloli mallakin jihar ta Kaduna akan farashin da bai kamata ba.
Kotu tace ya aikata laifinne a shekarar 2022.