
Rahotanni daga jihar Legas na cewa, Fadan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da gwamna Legas, Babajide Sonwo Olu ya zo karshe.
Gwamnan legas din ya musanta zargin cewa akwai wata rashin Jituwa a tsakaninsa da Tinubu inda yace Tinubu ubane sannan kuma shugabansa ne.
Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a Legas din bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasar Ranar Lahadi inda yace dama can babu wata rashin Jituwa a tsakaninsu.
An yi ganawar ne a gidan shugaban kasar dake Ikoyi. An fara zargin akwai wata kullalla tsakanin shugaba Tinubu da Gwamna Sonwo Olu ne bayan da shugaban ya kaddamar da Titin Legas zuwa Calabar amma ba’a ga Sonwo Olu a wajan ba.
Sannan a wajan wani taro, shugaban ya gaisar da kowa dake wajan amma bai gaishe da gwamnan Legas din ba.