Monday, February 16
Shadow

Fadar Shugaban asa ta zargi Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da bata mata suna ta hanyar yada labaran Karya

Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta zargi Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da yada labaran karya dan bata mata suna.

Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan.

Yace abinda ElRufai yake yi yana son ya kawar da hankulan mutanene daga kan zargin cin hanci da rashawa da ake masa a jihar Kaduna.

Kuma yana son jawo hankalin mutanen Najeriya ne akansa.

Ya kuma zargi malam da amfani da labaran karya wajan batawa gwamnati suna.

Gwamnatin ta kuma zargi ElRufai da kokarin kawo tsoro da tashin tashina a fadin Najeriya.

Yace kuma ElRufai na son mutane su rika ganin kamar ana son a zalinceshine.

Karanta Wannan  Labari Me Dadi: Shugaba Tinubu ya sa a rage farashin wankin Koda daga Naira Dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *