Thursday, June 5
Shadow

Fadar Shugaban Kasa ta karyata maganganun Adesina kan ci gaban Najeriya

Fadar Shugaban Kasa ta karyata maganganun Adesina kan ci gaban Najeriya

Fadar Shugaban Ƙasa ta karyata maganganun da aka danganta wa Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, inda ya ce halin da ‘yan Najeriya ke ciki a yanzu ya fi na shekarar 1960 muni.

Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin yada labarai , ya wallafa a shafinsa na X cewa Adesina ya dogara da wasu ƙididdiga “da ba su dace da bayanan da ake da su ba.”

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, “Babu wani mai lura da gaskiya da zai ce Najeriya ba ta samu ci gaba ba tun daga 1960. Yanzu haka, yayin da muke jiran sabon tsarin ƙididdigar GDP daga NBS, za mu iya cewa ba tare da jayayya ba cewa ya ninka na lokacin ‘yancin kan mu sau 50, ko ma sau 100.”

Karanta Wannan  YANZU YANZU: Wata kungiyar Matasan Arewa Masu goyon Bayan Bola Tinubu Wadda take da yawan Mabiya miliyan 100 ta yiwa Shugaban ƙasa Bola Tinubu Alƙawarin kawo Masa Miliyoyin kuri'un Matasan Arewa a kakar zaɓe Mai zuwa ta 2027

Onanuga ya zargi Adesina da yin magana “kamar ɗan siyasa irin su Peter Obi, ba tare da yin cikakken bincike ba kafin yin wannan magana da ba ta da sahihanci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *