
Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, ba zata yafewa Peter Obi ba saboda kalaman da yayi na amincewa da cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kawo Hari Najeriya.
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a rubutun da yayi a shafinsa na X inda yace ba zasu amince da kawo harin na Trump ba.
Peter Obi yace kamar mutum ne da iyalansa na fama da yunwa kawai sai wani ya kawo musu abinci, yace ai kamata yayi ya amince.
Yace to Najeriya abinda take bukata ne Amurka tace zata kawo mata ai kamata yayi kawai ta amince.