Wednesday, January 15
Shadow

Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Babban malamin Addinin Islama, sheikh Isa Ali Pantami ya yi martani kan faduwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi a wajan bikin ranar dimokradiyya.

Sheikh Pantami ya bayyana cewa, faduwar shugaban kasar bata da alaka da shugabanci kuma zata iya faruwa akan kowa. Ya bayar da shawarar cewa a rika kawar da akai akan irin wadannan labarai zai fi kyau.

“This can happen to any of us. It has nothing to do with governance. The earlier we ignore this kind of news, the better. May the Almighty make Nigeria a better place for us.”

Malam yayi martanine bayan da jaridar Vanguard ta wallafa labarin faduwar shugaban kasar.

Karanta Wannan  Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da 'Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

Saidai malam ya sha martani daga bakin wasu dake cewa bai yi magana akan kashe-kashen da akw yi a Arewa ba amma gashi yana kare shugaban kasa.

Waspapping dake amfani da sunan Sarki, wanda ya shahara wajan bayyana ra’ayi da kare muradun Arewa a Twitter ne ya fara magana inda yace cewa an kashe mutane 50 a Kankara amma malam bai yi magana ba sai akan faduwar shugaban kasa.

Karanta Wannan  Daga Yanzu Sarkin Musulmi Ba Shi Da Ikon Yi Wa Kowa Nadi, Cewar Gwamnatin Sokoto

Ya kara da cewa irin su Sheikh Pantami ne ya kamata ace suna kare muradun ‘yan Arewa.

“By the way, I don’t recall seeing a tweet from this man about the killing of 50 farmers in Katsina yesterday, but he has time to tweet about President Bola Ahmed Tinubu falling down.

These are the people who are supposed to speak in our interest.”

Wani me suna Ukasha Abdul Usman ya goyi bayan Waspapping da cewa:

Wani me sunan AK shima yace mutane 50 aka kashe amma baka yi kuka ba malam:

Karanta Wannan  Duk Wani Jami'in Zabe Da Ya Aikata Cin Hanci Da Rashawa Da Rashin Da’a Zai Fuskanci Hukunci --- INE
https://twitter.com/HassanHusseinY1/status/1800913523813331126?t=urp_S71_IrD1lM6CgZEG4w&s=19

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *