Wednesday, January 15
Shadow

Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji

Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji

… don Allah a yada (sharing) domin amfanar wadanda ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba
.
An karbo Hadisi daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: ranar daya ga watan zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya gafarta wa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) Zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da Shi.
.
(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) Ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada .
.
(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) Ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai karbi adduo’in sa.
.
(4) Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai kare shi daga talauci da musibu.
.
(5) Ranar biyar ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai kare shi daga munafunci ko azabar kabari.
.
(6) Ranar shida ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya Yi budin alkhairi ga Annabi (SAW). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai dube shi da rahama, kuma ba Zai azabtar da shi ba.
.
(7) Ranar bakwai ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Zai sa a rufe kofofin wuta, ba za a bude su ba har sai wadannan kwanaki goma sun wuce. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai rufe masa kofofi talatin na tsanani a rayuwar sa, a bude masa kofofi talatin na sauki.
.
(8) Ranar takwas ga Zulhijja ita ce ranar da ake cewa, ranar tarwiyya. Duk wanda ya azimci wannan ranar, babu wanda ya san adadin sa sai Allah.
.
(9) Ranar tara ga watan Zulhijja ita ce ranar hawan Arfa. Allah Yana gafartawa duk Alhazan da ke wurin Arfa. Wanda kuma ba ya wurin aikin Hajji, idan ya azimci wannan ranar, Allah Yana gafarta masa zunubansa na shekarar da ta gabata, da kuma shekarar da ke tafe.
.
(10). Ranar goma ga Zulhijja ita ce ranar layya. Duk wanda Allah Ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka dabbarsa, digon jini na farko da zai fara diga a kasa zai zama gafara gare shi da iyalin sa. An so wanda zai yi layya da wanda ba zai yi ba ya kame bakinsa sai bayan an dawo daga sallar idi, ya ci abinci ko wani abu daga cikin layyarsa. Allah Zai ba shi lada wacce ta fi Dutsen Uhud girma da nauyi. Kuma ana so ya raba naman sa kashi uku. Kashi na farko sadaka, kashi na biyu kyauta, kashi na uku kuma domin iyali.
.
Allah Ya ba mu Ikon azumtar dukkan wadannan ranakun, kuma Ya sada mu da falalar da Ya tanadar ga masu Ibada a wadannan ranaku. Amin.

Jama’a don Allah a yada (sharing) domin amfanar jama’ar musulmi.

Karanta Wannan  Sunayen maza masu dadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *