Thursday, January 9
Shadow

Farashin kayan Abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoman Arewa sun zabi kai kayan amfanin gonarsu kasashen waje

Rahotanni sun bayyana cewa ana hasashen farashin kayan abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoma a Arewa sun zabin kai kayan abincinsu kasashen waje su sayar maimakon sayarwa a gida Najeriya.

Manoma a jihohin Kaduna da Kwara sun koka da rashin amfanin gona me kyau saboda karancin ruwan sama da krkatar da kayan noman da ‘yan siyasa suka yi.

Saidai manoma a jihohin Jigawa, Kano da Yobe sun bayyana samun amfanin noma sosai irinsu Dawa, Wake, Masara, Gero da Sauransu.

Saidai sun bayyana cewa, mafi yawancin kayan amfanin nasu zasu kaisu jihohin wajene dan sayarwa.

Hakan a binciken jaridar Punchng ya nuna cewa, zai iya kaiwa ga hauhawar farashin kayan abinci a wannan shekarar.

Karanta Wannan  IMF ya nemi Tinubu ya tausaya wa talakawan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *