Idan a lokacin jinin hailarki ne farin ruwa mai kauri ke fita daga gabanki, to babu matsala.
Amma idan ba lokacin haila bane, zai iya zama matsalar rashin lafiya.
Fitar ruwa a gaban mace alamace ta lafiyar gaban watau farji.
Yawanci duk farin ruwan da zaki ga yana fita daga gabanki a lokacin jinin al’ada ba alama bace dake nuna akwai matsala ba, hakan na nuna al’aurarki ko gabanki bashi da matsala.
Amfanin wannan ruwa dake fitowa daga gabanki yana taimakawa fatocin dake cikin gabanki wajan yin laushi sosai a lokacin jinin al’ada da kuma lokacin da kike dauke da ciki.
Hakanan wannan ruwan yana fitar da duk wani datti dake gabanki kuma yana sa gabanki yayi laushi.
Saidai a wasu lokutan, farin ruwa me kauri na iya zama alamar rashi lafiya.
Masana kiwon lafiya sun ce a yayin da kike ganin wannan farin ruwa me kauri, idan kina son daukar ciki, daidai lokaci kenan da ya kamata a yi jima’i dan a lokacin kwayoyin daukar cikinki sun bayyana.
Shi wannan farin ruwa me kauri,muddin baya wari ko kuma baya nuna wasu alamomi to ba matsala bace.
Kawai dai zaki iya saka auduga a karkashinki dan kada ya rika bata miki wando ko kuma abinda ake cewa liner.
Hakanan ruwan idan ya kasance me kalar madara ne shima duk ba matsala, matukar dai baya wari ko kuma wasu abubuwa na daban.
Saidai idan ya fara canja kala zuwa Gray/Grey ko kalar toka wanda ba me duhu ba ko kuma ya fara wari kamar kifi to akwai matsalar rashin lafiya.
Idan wannan ruwa ya zamana yana da yauki, musamman idan bayan an gama jinin haila ne, to zai zama yana hana ruwan maniyyi shiga cikin mahaifa, hakanan zai hana duk wata cuta ko infection shiga cikin al’aurarki.
Idan kuma ya zamana wannan ruwa me kauri fari kuma yana fita dunkule-dunkule to wannan alamace ta infection.
Me infection zata rika ganin ruwa me kauri a dunkule yana fita.
Za’a iya ganin farin ruwa wanda zai iya komawa kalar Yellow ruwan dorawa ko kalar Green watau koriya.
Idan wari yana fitowa daga al’aurar.
Kaika yi a waje ko a cikin al’aurar.
Za’a iya ganin Kumburi ko kan al’aurarki zai yi jaa.
Za’a iya jin zafi lokacin fitsari.
Za’a iya jin zafi lokacin jima’i.
Idan aka ji wadannan alamomi to alamace an kamu da cutar infection sai a nemi magani.
Akwai magunguna na gargajiya dana likita da kuma wanda ake hadawa a gida.
Akwai magungunan da ake hadawa a gida da muka yi bayaninsu