Wednesday, January 15
Shadow

Gajerun kalaman soyayya na barka da safiya

Barka da safiya matata insha Allah, wataran da hannuna zan tasheki daga bacci.

Barka da safiya matata insha Allah, wataran a gado daya zamu kwana.

Barka da safiya matata insha Allah, wataran akan kirjina bacci zai kwasheki.

Barka da safiya matata insha Allah ina miki fatan samun alkhairin wannan yini.

Salam Masoyiyata, na kwanta da sonki na tashi dashi, ina fatan kema kin tuna dani.

Salam Masoyiyata ina sonki a ko da yaushe, yanzu ma sonki ne ya tasheni, ina miki fatan alkhairin wannan jini.

Masoyiyata na yi mafarkinki, kema kin yi mafarkina kuwa?

Salam Farkawa na yi, na yi sallar Asuba, na yi zikirin safiya, na dauko abincin kari zanci, sai naji bana jin dandanonsa a bakina, ina ta tunane-tunane sai na tuna ashe muryarki ce da ban ji ba.

Karanta Wannan  Kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin

Salam Inawa ‘yar Alkhairi fatan barka da safiya.

Salam Ance wai idan kana son ganin munin mace ka ganta a lokacin data tashi bacci, ni kuwa tawan ko ba hoda kyanta na asaline, Barka sa safiya.

Salam Barka da safiya, Ina sonki so na hakika.

Kin Tashi lafiya habibiyata?

Ina son ki zamo abinda na fara karyawa dashi. Barka da safiya.

Salam Zan so in ga ranar da zamu ci abincin karin aafe tare, Barka sa safiya.

Salam Ina sonki da safe da yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *