Wednesday, January 15
Shadow

Gajerun sakonnin soyayya

Ga Gajerun sakonnin soyayya masu rasha jiki kamar haka:

Duk yadda zuciyata ke tafasa da na ganki sai inji ta yi sanyi.

Kece karin kumallo na, ko da na ci abinci in banji muryarki ba yunwa bata sakina.

Taba waya akwai dadi amma ni hira dake yafi min dadi.

Ko a indiya sai an bincika kamin a samu me kyau irin naki.

Bansan akwai mata masu kama da larabawa ba a kasar mu sai da na hadu dake.

Bincikena ya kare ban gano mace me kwarjini irin naki ba.

Kanshinki na kai ni Duniyar da ban tantance ba.

Nasan ‘Ya’yanmu zasu zama kyawawa saboda mun dace da juna.

Karanta Wannan  Ya ake yiwa saurayi fira

Na yi babbar sa’a idan na sameki a matsayin mata, dan kuwa ‘ya’yana zasu samu tarbiyya.

Hankalinki da nutsuwarki na kara sawa in soki.

Kina da kamun kai, kina da girmama mutane, kin iya kalaman soyayya, Allah yawa iyayenki Albarka dan sun baki tarbiyya me kyau.

Idan aka ajje min kudi dake, ke zan dauka.

Babu abinda zai sa in daina sonki.

Jin Muryarki nasa in samu nustuwa.

Nutsuwata itace in ji muryarki kamin in kwanta hakanan in jita bayan na tashi da safe.

Idan naci abinci ni kadai ina koshi, amma idan na ci abinci kina gabana sai inji na gamsu kamar bazan kara jin yunwa ba.

Karanta Wannan  Sunayen soyayya na mata

Kallonki na rikitamin lissafi.

Bansan me zaki min inji zuciyata ta canja akan sonki ba.

Idan ina tafiya dake a titi ji nake kamar wani gwamna.

A duk sanda bama tare, gabana faduwa yake saboda kar wani yamin kwacenki

Ina sonki ba misali a zuciyata.

A mafi yawan lokuta nakan yi shiru ba tunanin komai nake ba sai ke.

Randa kika zama matata bansan wane irin jin dadi zan yi ba.

Ina sonki, ina son in ta kallon fuskarki, ina son inta jin muryarki, ina son inta zama tare da ke, ina son ki rika min kallon soyayya.

Naji mawaka da yawa sun yabi masoyansu amma har yanzu banji yabon da ya cancanta in dangantaki dashi ba dan duk kalamansu basu bayyana irin son da nake miki ba.

Karanta Wannan  Labarin soyayya

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *