
Rahotanni sun ce gidajen saye d man fetur akalla 4900 ne suka kulle a fadin kasarnan saboda rashin tabbas na kasuwar man fetur din.
‘Yan kasuwar da yawa basa iya sayen tankar mai, inda a yanzu sai ka da an hada kudi na ‘yan kasuwa biyu zuwa uku kamin su samu damar sayen tankar man fetur daya wadda a baya cikin sauki mutum daya ke iya sayenta.
Daga watan Janairu na shekarar 2025 zuwa Afrilu matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin ta sau 6 inda ya fara a Naira 950 har ya sakko zuwa 835.
‘Yan kasuwar da basu ma da kudin da za’a yi wannan hadaka dasu dole tasa sun rufe gidajen man fetur din.
Bayan zuwan Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, Ta cire tallafin man fetur wanda hakan yasa farashin ya koma hannun ‘yan kasuwa.