Rahotanni sun bayyana cewa yawan wanda suka mutu a ci gaba da yaduwar mahaukaciyar gobarar garin Los Angeles na kasar Amurka na ci gaba da karuwa.
Zuwa yanzu mutane 16 ne hukumomi suka tabbatar da cewa, sun mutu a gobarar.
Kamfanin dillancin labaran AP yace biyar daga cikin wadanda suka mutu a unguwar Palisades ne sai 11 kuma a unguwar Eaton sannan kuma mutane 13 sun bace ba’a san inda suke ba.
Zuwa yanzu gidaje dubu talatin da biyar ne suke cikin duhu babu wutar lantarki sanadiyyar gobarar.
Sama da masu aikin kashe gobara dubu goma sha hudu ne ke ta aiki ba dare ba rana dan hana gobarar yaduwa.
Hutudole ya kawo muku cewa, yawan wanda ke kashe gobarar sun yi kadan ta yanda saida aka fito da masu laifi daga gidan yari dan su taimaka