Wednesday, January 15
Shadow

Goron Sallah: Gwamnan Sokoto ya bai wa ma’aikatan jihar naira 30,000

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da bai wa ma’aikatan jihar naira 30,000 a matsayin goron sallah.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan muhalli na jihar, Nura Shehu ya aike wa BBC, ta gwamnan jihar ya amince da bai wa duka ma’aikatan jihar da ƙananan hukumomi da masu fansho goron sallar.

Sanarwar ta ƙara da cewa su ma ma’aikatan wucin gadi masu karbar alawus-alawus za su amfana da goron sallar.

”Rukuni na farko ya haɗa da ma’aikatan Jiha, da na ƙananan hukumomi za su karɓi naira 30,000 a matsayin goron Sallah”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce ”rukuni na biyu da ya ƙunshi masu karɓar fansho da masu karɓar alawus-alawus a ƙananan hukumomi da kuma masu karɓar alawus-alawus a hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko waɗanda za su karɓi naira 20, 000 a matsayin goron sallar”.

Karanta Wannan  Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Ahmad Jalam ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Misau-Darazo ranar Asabar a cewar gwamnatin jihar

Tuni dai dai gwamnan jihar ya bayar da umarnin biyan albashin watan yuni ga ma’aikatan jihar a wani ɓangare na rage musu raɗaɗi gabanin bukukuwan babbar sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *