Sunday, July 21
Shadow

Da Duminsa: ‘Yansanda sun haramta hawan Sallah a Kano

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.

”Haka kuma an haramta duka nau’ikan hawan sallah a lokacin bukukuwan babbar sallah da ke tafe”, in ji sanarwar.

‘Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.

Karanta Wannan  Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Haka kuma ‘yan sandan sun shawaraci mazauna jihar da su gudanar da sallar idinsu cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka saba, ba tare da tashin hankali ba.

”Don haka muna kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusanci”, in ji sanawar.

Hakan na zuwa ne dai bayan da jama’a suka zura ido suna jiran ganin wanda zai yi hawan babbar sallah a jihar, kasancewa akwai ana taƙaddama mai ƙarfi game da sarautar Kano, lamarin da yanzu haka ke gaban ƙuliya.

A ranar 23 ga watan Mayun 2024 ne dai, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗa Muhammadu Sanusi II, a matsayin sarkin Kano na 16, bayan sauke Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma rushe ƙarin masarautun da gwamnatin Ganduje ta yi a shekarar 2019.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka kulle Gidan Dabo

A yau ne dai wata babbar kotun tarayya a Kano ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan rikicin masarautar Kanon, musamman kan abin da ya shafi kare hakkin ɗan’adam bisa dogaro da sashe na 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Alƙalin kotun, mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke jihar, ya yanke hukuncin cewa tsohon sarki Aminu Ado Bayero na da damar a saurare shi a kotu.

Sai dai alkalin ya ce ba magana ce a kan cancantar majalisar dokokin jihar na sauya dokar masarautun jihar ko kuma a’a ba.

Alƙalin ya bayyana cewa kotun ba ta ƙalubalantar damar da gwamnatin jihar ke da shi na naɗawa ko sauke sarki.

Karanta Wannan  Kotu na da hurumin sauraron ƙara kan masarautar Kano

Aminu Babba Danagundi ne ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar gyaran dokar masarautun jihar da majalisar dokokin jihar ta yi cikin watan da ya gabata.

Inda kotun ta bayar da umurnin tsayawa kan matsayin da ake kafin yin gyaran, har zuwa lokacin da za ta yanek hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *