Sunday, May 25
Shadow

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna Alhininsa da mika ta’aziyya ga iyalan wanda suka ràsù a hadarin mota a Danbatta

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa tare da ta’aziyya ga al’ummar ƙaramar hukumar Dambatta bisa rasuwar mutum biyar yan yankin sakamakon haɗarin mota ranar Lahadi.

Hadarin dai ya faru kilometer bakwai kafin shiga garin Dambatta lokacin da mutanen ke dawowa daga jihar Bauchi bayan sun raka amarya.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai yayan Alhaji Surajo guda biyu da kuma yayan kaninsa Alhaji Salisu Dan Raino guda uku.

Sanarwar daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta rawaito Abba Kabir Yusuf na bayyana rashin a matsayin na al’ummar Kano gaba ɗaya tare addu’ar Allah ya ji ƙan su ya bai wa iyalansu hakuri.

Karanta Wannan  Hotunan Sabon Jirgin Saman Shugaban Kasa Bola Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *